31 Disamba 2021 - 13:09
​Afganistan: Ghani, Ya Dora Alhakin Rugujewar Gwamnatinsa Ga Amurka

Tsohon shugaban kasar Afganistan Ashraf Ghani ya zargi Amurka da rugujewar gwamnatinsa, yana mai cewa Washington ta mayar da shi gefe guda a lokacin da ake tattaunawa da kungiyar Taliban.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Ya kara da cewa "An yi min fenti baki daya... ba a taba ba mu damar zama da su (Taliban) ba in ji Ghani yayin wata hira da shirin BBC na ranar Alhamis.

Amurka ta cimma matsaya da kungiyar Taliban a watan Fabrairun 2020 kan janye sojojin Amurka 12,000 daga Afganistan, kan musayar kungiyar Taliban ta dakatar da kai hare-hare kan dakarun kasashen waje.

Yarjejeniyar da Amurka da Taliban suka cimma, ta samo asali ne sakamakon tattaunawar zaman lafiya da aka yi a Doha babban birnin Qatar, inda aka cire gwamnatin Afghanistan daga cikinta.

Gwamnatin Afghanistan ta ruguje a ranar 15 ga watan Agusta, sakamakon kwace yankunan kasar da kungiyar Taliban ta yi, kuma a ranar 7 ga watan Satumba Taliban ta sanar da kafa gwamnatin rikon kwarya a Afghanistan.

342/